Bala Mohammed ya bukaci kafafen yaɗa labarai su guji labaran karya
By Abdulhakeem Sunusi Danbakano Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihanci, daidaito da gaskiya wajen yaɗa labarai, domin karfafa dimokuradiyya da yaki da labaran karya, musamman yayin da ake tunkarar babban zaben 2027. Gwamnan ya ce kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a da kuma samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da zabuka cikin kwanciyar hankali. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi ta kashe sama da Naira biliyan uku wajen zamanantar da gidajen rediyo da talabijin na jihar, domin inganta ayyukansu da kuma basu damar gudanar da watsa shirye-shiryen zamani. A nata bangaren, kungiyar Society of Nigerian Broadcasters (SNB) ta bukaci masu watsa shirye-shirye da su kara amfani da fasahar zamani wajen tabbatar da cewa rahotannin zabe sun kasance sahihai, cikin sauri kuma masu inganci. Kungiyar ta ce amfani da fasaha yadda ya kamata zai taimaka wajen rage yada bayanan bogi tar...