PDP ta rushe shugabancin jam’iyyar na Kano

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano



Jam’iyyar PDP ta rushe shugabancin jam'iyyar na Jihar Kano, tare da sauke shugaban jam’iyyar na jihar, Dr Bello Gambo Bichi.

Shugabancin jam'iyyar  ne ya ɗauki matakin, wanda ya fara aiki nan take, kamar yadda wata wasiƙa mai kwanan wata 24 ga Satumba 2026 ta bayyana.

Jam’iyyar ta ce rushewar ta shafi shugabancin jihar ne kawai, yayin da kwamitocin jam’iyyar na ƙananan hukumomi da mazabu ba su cikin matakin.

PDP ta kuma umarci Kwamitin Rikon Kwarya na Arewa maso Yamma da ya kula da harkokin PDP a Kano har sai an zaɓi sabon Kwamitin Ayyuka na Jihar.

Da yake magana kan matakin, Bichi ya ce ya amince da rushewar a matsayin sadaukarwa domin sulhunta ‘yan jam’iyyar da ƙarfafa PDP a Kano.

Ya ce matakin na daga cikin sharuɗɗan sulhun da aka cimma, musamman bayan sauya tsohon ɗan takarar gwamnan PDP, Dalhatu, da Muhammad Abacha a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Bichi ya ce ya amince da sauyin ne saboda burin sake haɗa kan jam’iyyar da kuma ƙara mata ƙarfi gabanin zaɓe.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration