Kuliyan Zazzau da Gudummawarsa ga Al'ummar Daukacin Kasar Zazzau
Daga Abdul-Azeez Suleiman A cikin al'ummar Zazzau, sunan Justice Ishaq Usman Bello ya zama abin koyi da girmamawa. A matsayin mai shari'a, ya kasance mai adalci da tsananin kulawa da hakkin kowa da kowa. Amma abin da ya fi daukar hankali shine yadda ya yi amfani da matsayinsa don inganta rayuwar matasa da marasa galihu a cikin al'ummar sa. A mahaifarsa Tukur-Tukur, Justice Bello ya kasance mai tasiri wajen kafa sabbin hanyoyin samun aiki da tallafi ga masu bukata, wanda hakan ya jawo hankalin al'ummar Zazzau baki daya. Justice Ishaq Usman Bello ya fahimci cewa matasa suna da matukar bukatar tallafi da jagoranci a zamanin yau. A cikin shekaru masu yawa na aikinsa, ya kafa shirin bayar da guraben aiki ga matasa sama da hamsin a ma'aikatu daban-daban na gwamnatin jihar. Wannan shiri ya ba da dama ga matasa su samu ilimi da kwarewa a fannoni masu yawa, wanda hakan ke kara musu kwarin gwiwa da kuma inganta rayuwarsu. Ta hanyar wannan shiri, Justice Bello ya ...