Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati da su guji daukar nauyin mutane zuwa Makka ko Kudus da kudaden da aka sace daga dukiyar al’umma.

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano



Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ya yi wannan gargadin ne a ranar Laraba yayin bude taron masu ruwa da tsaki na majalisar addinai ta Najeriya (NIREC) a Abuja.

Sarkin ya ce bai kamata a yi amfani da kudaden rashawa wajen gudanar da ayyukan ibada ba, yana mai kira ga shugabannin addinai da su hada kai da hukumomin yaki da cin hanci wajen dakile rashawa.

Ya kuma bukaci EFCC ta hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen cin hanci ba tare da la’akari da addininsa ko matsayinsa na siyasa ba.

Sarkin ya kuma gargadi malamai da su guji kalaman da za su haddasa rarrabuwar kawuna, musamman a lokacin zabuka, inda ya bukace su da su rika yi wa shugabannin kasa addu’a.

A nasa bangaren, Shugaban kwamitin shawara kan yaki da cin hanci tsakanin Addinai, Farfesa Adedibu Ojerinde, ya ce an samar da littattafan yaki da rashawa domin taimakawa malamai wajen isar da sakonnin yaki da cin hanci a masallatai da coci-coci.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration