Zargin barkewar kwalara: Amnesty ta bukaci a ayyana dokar ta-baci a gidan yarin Kurmawa dake Kano

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano


Ƙungiyar Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gaggauta ayyana dokar ta-baci a gidan yarin Kurmawa da ke Kano, sakamakon mutuwar aƙalla fursunoni shida cikin mako guda, bisa zargin barkewar cutar kwalara.

Ƙungiyar ta ce wasu fursunoni na ci gaba da karɓar magani, yayin da ta yi gargadin cewa rashin ɗaukar matakin gaggawa na iya haifar da ƙarin asarar rayuka.

A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, Amnesty International ta buƙaci a garzaya da fursunonin da ke cikin mawuyacin hali zuwa asibitoci domin samun kulawar da ta dace.

Ta kuma yi gargadin cewa adadin waɗanda suka mutu ka iya kasancewa ya fi haka, yayin da ake zargin cutar na ci gaba da yaɗuwa tsakanin fursunonin, musamman waɗanda ke tsare yayin da suke jiran shari’a.

Amnesty ta ce rashin gaggauta ɗaukar mataki domin dakile cutar na iya haifar da take haƙƙin rayuwar fursunoni, wanda ke iya zama babban take haƙƙin ɗan Adam a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma soki yanayin da ake tsare da fursunoni a gidajen yari na Najeriya, musamman waɗanda ke ɗaukar shekaru suna jiran shari’a.

Ta ce da dama daga cikinsu na rayuwa a cikin cunkoson ɗakunan tsare marasa tsafta, ba tare da isasshen abinci da kulawar lafiya ba.

Amnesty ta ƙara da cewa wasu daga cikin fursunonin na iya shafe tsawon rayuwarsu a gidan yari ba tare da an same su da laifin da aka tuhume su da shi ba.

Ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakan gaggawa tare da yin gyare-gyare domin tabbatar da cewa yanayin tsare fursunoni ya dace da ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam da kuma ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration