Atiku ya nada El-Rufai cikin kwamitin yakin neman zabensa
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nada tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a matsayin mamba a kwamitin yakin neman zabensa. Atiku ya sanar da nadin ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Nadin na zuwa ne a lokacin da El-Rufai ke tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume daga gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna. Rahoton jaridar Daily Trust ya ce tsohon gwamnan yana tsare tun watan Fabrairu
Comments
Post a Comment