Kwamitin yaƙin neman zaɓe: Ƙungiyar OK Movement ta jaddada ra'ayin ta duk da ƙin amincewar Obi
By Abdulhakeem Sunusi Danbakano
Ƙungiyar Obi-Kwankwaso (OK Movement) ta sake jaddada cewa ƙungiya ce mai zaman kanta, tana kuma da hurumin kafa da tafiyar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na kanta.
Wannan na zuwa ne bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa ƙungiyoyin da ke mara wa jam’iyyar baya bai kamata su kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe na kansu ba tare da amincewar shugabannin Obi da Kwankwaso ba.
Sai dai Darakta-Janar na OK Movement, John Ughulu, ya ce tsarin shugabanci da harkokin cikin gida na ƙungiyar ba ya buƙatar amincewar shugabancin NDC.
Ughulu ya bayyana cewa NDC tana da ’yancin gudanar da tsarinta na yaƙin neman zaɓe, yayin da OK Movement ma take da ’yancin tafiyar da nata harkoki bisa doka.
Ya ce ƙungiyar ba za ta amince da duk wani yunƙuri na rushewa ko tsoma baki cikin tsarin shugabancinta ba, yana mai cewa matsayinsu ba na neman faɗa ba ne, illa dai kare ’yancin ƙungiyar.
Ya ƙara da cewa OK Movement za ta ci gaba da aiki tare da NDC, musamman wajen tattara magoya baya daga matakin ƙasa, amma ba za ta yi watsi da ƙa’idojinta da tsarin shugabancinta ba.
Comments
Post a Comment