EFCC ta fara sa ido kan yadda shugabannin ƙananan hukumomi ke kashe kuɗaɗen al’umma

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano


Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC) ta ce ta fara faɗaɗa ayyukanta zuwa ƙananan hukumomi domin sa ido kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen al’umma, musamman ganin yadda ƙananan hukumomin ke ƙara samun kuɗaɗe daga Gwamnatin Tarayya.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja, yayin taron farko na shekara-shekara na shugabannin ƙananan hukumomi da majalisun sarakunan gargajiya.

A cewar Olukoyede, hukumar za ta ƙara mayar da hankali kan yadda ake amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa an kashe su bisa ƙa’ida kuma domin amfanin al’umma. Jaridar Daily Nigerian ce ta ruwaito.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration