Gwamnan jihar Gombe ya nada sabbin Kwamishinoni 3 da masu taimaka masa 6

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano
Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya amince da nadin sabbin Kwamishinoni guda uku, da Masu Ba da Shawara na Musamman biyu, da kuma Manyan Mataimaka na Musamman hudu.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce gwamnan ya tura sunayen kwamishinonin da aka zaba zuwa Majalisar Dokokin Jihar Gombe domin tantancewa da amincewa.

Kwamishinonin da aka nada sun hada da Dr Ahmed Wali Doho, Nasiru Adamu Degri da Dr Muhammad A. Bello.

Haka kuma, gwamnan ya nada Abdulmalik Jibrin da Mohammed Nuhu a matsayin Masu Ba da Shawara na Musamman.

Sauran wadanda aka nada su ne Jibrin M. Ali, Sadiq Abubakar, wanda aka fi sani da BB Kumo, John Launa da Danlami Sanda, a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman kan harkokin siyasa da hulda da al’umma.

Sanarwar ta ce nadin ya fara aiki nan take, sai dai nadin kwamishinonin uku na jiran amincewar Majalisar Dokokin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce nadin na da nufin inganta tafiyar da gwamnati da kuma taimakawa wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban jihar.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration