A 2016 na kusa sauya sheƙa zuwa Liverpool - Mbappé
By Abdulhakeem Sunusi Danbakano
Shahararren ɗan wasan Faransa da Real Madrid, Kylian Mbappé, ya bayyana cewa ya kusa komawa kungiyar Liverpool a shekarar 2016, amma daga bisani ya ƙi amincewa da tayin.
Mbappé ya bayyana hakan ne a wata hira da The Athletic, inda ya ce Liverpool ta yi ƙoƙarin ɗaukar sa ne lokacin da yake taka leda a Monaco.
Ya ce mahaifiyarsa ta kasance mai sha’awar tsohon kocin Liverpool, Jürgen Klopp, kuma tana son ya koma ƙungiyar.
Sai dai ya ce ya zaɓi ya ci gaba da zama a Faransa saboda yana son taka leda a garinsu na Paris, kuma bai shirya barin ƙasarsa ba a lokacin.
Ya bayyana cewa mahaifiyarsa har ta je Liverpool domin ganin birnin da filin wasa na Anfield, inda ta kuma gana da wasu jami’an ƙungiyar.
A cewar Mbappé, mahaifiyarsa ta ji daɗin ƙungiyar sosai, inda ta yi imanin cewa Liverpool ƙungiya ce mai kyakkyawar alaƙa da magoya bayanta.
Ya kuma bayyana cewa ya gana da Jürgen Klopp a lokacin da Liverpool ke ƙoƙarin shawo kansa ya koma ƙungiyar.
Sai dai duk da ƙoƙarin Liverpool da kuma muradin mahaifiyarsa, Mbappé ya zaɓi komawa Paris Saint-Germain (PSG) a shekarar 2017.
Ya ce kasancewarsa ɗan asalin Paris da kuma burinsa na zama tauraro a garinsu ne suka sa ya zaɓi PSG.
Mbappé ya koma PSG daga Monaco a matsayin aro a 2017, kafin daga bisani yarjejeniyar ta koma cikakkiyar cinikayya kan kuɗin Yuro miliyan 180.
Ya shafe shekaru bakwai a PSG, inda ya zama ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin ƙungiyar, kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2024.
Comments
Post a Comment