UNGA: ‘Tinubu na guje wa Amurka ne saboda tsoron kamu’ - Okonkwo

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano


Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaɓen tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da guje wa zuwa Amurka saboda tsoron yiwuwar kama shi.

Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Prime Time na Arise News, yana mayar da martani kan rashin Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 (UNGA) da ake gudanarwa a New York.

Ya ce Tinubu bai halarci taron UNGA da kansa ba tsawon shekaru uku a jere, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ke wakiltar Najeriya a wannan karon.

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zargin, tana mai cewa rashin Tinubu ba shi da alaƙa da wata barazanar kama shi, domin yana gudanar da ayyukan gwamnati daga wajen ƙasar.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya kuma ce batun bayanan da hukumomin Amurka ke riƙe da su game da Tinubu, wanda ya shafi wani al’amari na kwace kuɗi a shekarar 1993, rikicin samun bayanai ne ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act, ba shari’ar laifi ba.

Jakadan Najeriya  a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce babu wata sanarwa daga gwamnatin Amurka da ta nuna cewa an hana Tinubu shiga ƙasar ko kuma yana fuskantar barazanar kama shi.

Fadar Shugaban Ƙasar ta ce Tinubu ya tafi ƙasar waje tun ranar 30 ga Agusta, inda ya ziyarci Faransa tare da gudanar da wasu taruka, kafin ya wakilta Shettima a taron UNGA.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration