Tsohon ɗan wasan Super Eagle Troost-Ekong ya musulunta
Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya karɓi addinin Musulunci bayan ya karanta Kalmar Shahada a birnin Doha na Qatar.
Jaridar Al-Arab ta Qatar ce ta rawaito cewa ɗan wasan ya bayyana musuluntarsa ne bayan ya furta kalmomin Shahada guda biyu.
Wani bidiyo da ke nuna Troost-Ekong yana karanta Shahada ya bazu a kafafen sada zumunta, yayin da malamin Musulunci, Dr Muhammad Salah, ya wallafa bidiyon a Facebook, yana mai bayyana cewa ɗan wasan ya musulunta.
Troost-Ekong mai shekara 33 a yanzu yana taka leda a ƙungiyar Al-Ahli ta Qatar, wadda ya koma a watan Janairun 2026 daga Al-Kholood ta Saudiyya.
Ya buga wasanni sama da 70 da tawagar Najeriya, kuma ya kasance cikin tawagar da ta kai wasan ƙarshe na gasar AFCON 2023 a Côte d’Ivoire, inda aka ba shi kyautar gwarzon ɗan wasa na gasar.
Comments
Post a Comment