Atiku ya baiwa iyayen mahaƙa ma'adanai 37 da suka mutu a hannun NSCDC tallafi Naira miliyan 20
By Abdulhakeem Sunusi Danbakano
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga iyalan mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ne, waɗanda suka mutu a hannun jami’an Hukumar Tsaron Farar Hula ta Ƙasa (NSCDC) a Minna, Jihar Neja.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Talata, yayin da ya kai ziyara ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma waɗanda su ka tsira daga faruwar lamarin.
Ya kuma ziyarci Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, da kuma tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), a lokacin ziyarar da ya kai jihar.
A cwata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Hulɗa da Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana mutuwar matasan a matsayin abin takaici da ke sake tunatar da yadda matasan Najeriya da ke ƙoƙarin neman ba kan su ke cikin mawuyacin hali sakamakon tsananin matsin rayuwa.
Ya ce Najeriya ba za ta iya tabbatar da makomarta ba tare da ta zuba jari da wajen matasa, faɗaɗa damar samun ayyukan yi da kuma ba su damar gudanar da sana’o’i na halal da masu amfani ba.
Atiku ya ce abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne bayanin da ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ya ba shi, inda ya ce sama da mutane 68 da ake tsare da su an cusa su cikin wani ƙaramin ɗaki, inda a haka da dama suka mutu.
Comments
Post a Comment