Oyegun ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan goyon bayan APC a 2023

By Abdulhakeem Sunusi Danbakano



Tsohon gwamnan jihar Edo, kuma jigo a jam’iyyar ADC, Cif John Odigie Oyegun, ya nemi afuwar ’yan Najeriya bisa goyon bayan da ya bai wa jam’iyyar APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.

Oyegun, wanda ya taɓa zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa daga 2015 zuwa 2019 kafin ya koma ADC a shekarar 2026, ya ce ’yan Najeriya na shan wahala sakamakon abin da ya kira kuskuren zaɓen da aka yi a 2023.

Ya bayyana hakan ne a birnin Benin yayin wani taron da ADC ta shirya domin tarbar ɗan takararta na mataimakin shugaban ƙasa, Rotimi Amaechi.

Oyegun ya ce zaɓen 2027 wata dama ce ga ’yan Najeriya domin gyara kuskuren da aka yi a baya da kuma samar da ci gaba a ƙasar.

Ya ce ADC na shirin gabatar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da Amaechi a matsayin ’yan takararta domin ceto ƙasar daga matsalolin da take fuskanta.

Comments

Popular posts from this blog

Nuhu Bamalli Polytechnic Gets NCCE Approval, Begins Admission into Expanded NCE Programmes

Zazzau Mourns: Eze Ndi Igbo of Zazzau's Burial Brings City to Standstill

KADVS assures residents of safety during Christmas, New Year celebration