Hajjin 2027: Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujeru 10,00
By Abdulhakeem Sunusi Danbakano
Hukumar alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ce Saudiyya ta ƙara wa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027 da 10,000, lamarin da ya ɗaga adadin kujerun ƙasar daga 50,000 zuwa 60,000.
NAHCON ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da na hukumar, Shafii Mohammed, ya fitar ranar Alhamis.
A cewar hukumar, an ware kujeru 7,500 daga cikin ƙarin adadin ga hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi, yayin da aka bai wa kamfanonin shirya aikin Hajji guda bakwai kujeru 2,500.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya gode wa gwamnatin Najeriya da hukumomin Saudiyya bisa ƙarin kujerun, yana mai cewa za a rarraba su cikin gaskiya da bin dokokin Najeriya da Saudiyya.
Hukumar ta ce ƙarin kujerun ya biyo bayan tattaunawar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Saudiyya.
Comments
Post a Comment